To sai dai daya daga cikin ‘yan uwan matasan Abdullahi Umar Kawoje ya shaida wa RFI hausa cewa matasan ba su da alaka da Boko Haram kuma suna da sana’ar hannun da su ke yi a birnin Legas.
Kawoje ya kara da cewa an kama matasan ba tare da wani makami a jikinsu ba kuma akasarin su ba su kai shekarun balaga ba. 289